28 Mayu 2020 - 05:07
Shugaban Kasar Sudan Ya Tabbatar Da Batun Ficewar Rundunar MDD Daga Kasar

Shugaban kasar Sudan kuma shugaban majalisar koli ta gudanarwan kasar, Abdul Fattah Alburhan ya tabbatar da cewa rundunar MDD dinkin duniya da ke yankin Darfur na kasar, wacce ake kira UNAMID za ta fice daga kasar a karshen wannan shekarar.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Sudan kuma shugaban majalisar koli ta gudanarwan kasar, Abdul Fattah Alburhan ya tabbatar da cewa rundunar MDD dinkin duniya da ke yankin Darfur na kasar, wacce ake kira UNAMID za ta fice daga kasar a karshen wannan shekarar.

Jaridar Sudan Tribune ta nakalto majiyar fadar shugaban kasar tana cewa, a jiya talata ce Alburhan ya zanta da Tibor Nagy mataimakin saktaren harkokin wajen kasar Amurka kan lamuran Afrika da kuma Jakadan Amurka a kasar Sudan Donald Booth, a lokaci guda, inda suka amince da batun ficewar rundunar ta UNAMID daga kasar ta Sudan a cikin watan Octoba mai zuwa.

Kafin haka dai Abdulfattah Alburhan ya bayyan rashin amincewarsa da kara tsawaita wanzuwar sojojin na MDD a kasar, a karshen wa’adin zamanta a kasar a wannan shekara ta 2020.

Kafin haka dai, a zaman kwamitin tsaro na MDD a ranar 26 ga watan Afrilun da ya gabata, kasashen Amurka da Burtaniya sun bukaci a tsawaita zaman rundunar ta UNAMID a kasar Sudan, banda haka sun bukaci a kara mata da ‘yansanda don kare lafiyar ‘yan gudun hijira a yankin Darfur na kasar ta Sudan.


/129